Iran ta sake kulle Mashigar Hormuz
April 18, 2026
Talla
Gwamnain Tehran ta ce ta dauki matakin sake kulle Mashigar Hormuz ne yayin da Amurka ke ci gaba da toshe tashoshin ruwanta. Sanarwar hakan na zuwa ne bayan da Shugaba Trump ya ce ba za a sassauta takunkumin ga Iran ba, har sai Iran din ta amince da wasu shirye-shirye ciki har da shirinta na Nukiliya.
Karin bayani: Iran ta sanar da bude mashigar Hormuz
Sai dai duk da fargabar da ake da ita, jami'ai a Pakistan na cewa Amurka da Iran na kara matsawa ga cimma yarjejeniya kafin ranar 22 ga wannan watan na Afrilu, da ke zama wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi da aka cimma.