Iran ta saki 'yar gwagwarmaya Narges Mohammadi daga kurkuku
December 4, 2024A Larabar nan ce Iran ta saki 'yar gwagwarmayar nan Narges Mohammadi da ta taba lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel daga kurkuku, domin zuwa a duba lafiyarta, kamar yadda mai gidanta Taqi Rahmani ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Karin bayani:Ana gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Iran
Daga cikin laifukan da suka sanya gwamnatin Iran daure Narges Mohammadi akwai yada farfagandar kin jinin gwamnatin, da sauran laifuka.
Karin bayani:Iran na azabatar da wata 'yar fafutuka
Wani sako da lauyanta mai suna Mostafa Nili ya wallafa a shafinsa na X a yau din nan, ya ce ofishin mai gabatar da kara na Iran ne ya sahale sakin nata na tsawon makonni uku, bayan karbar rahoton gwaje-gwajen da likitoci suka yi mata, da suka tabbatar da cewa hakika tabarbarewar lafiyarta ta yi kamarin da ya zama wajibi a bata kulawa ta musamman.