1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta bude mashigar Hormuz

April 17, 2026

Trump ya ce ''ya godewa Iran'' kan daukar matakin, sai dai ya jaddada cewa takunkumin da ya kakaba na tsoshe tashoshin jiragen ruwanta na nan daram har sai an kammala tattaunawa.

Vereinigte Arabische Emirate Khor Fakkan 2026 | Öltanker in der Straße von Hormus
Hoto: Altaf Qadri/AP Photo/picture alliance

Iran ta sanar da bude mashigar Hormuz gaba daya a wannan Juma'a, bayan fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, lamarin da ya haifar da kyakkyawan fatan kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya.

Tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon ta fara aiki

Sanarwar ta Teheran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da ita, ta haifar da raguwar farashin mai da kashi 10 cikin 100 da kuma farfadowar kasuwannin hannayen jari a Turai, bayan makonni biyar na yaki da ya yi mummunar illa ga tattalin arzikin duniya.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce ''ya godewa Iran'', sai dai ya jaddada cewa takunkumin da ya kakaba mata na tsoshe tashoshin jiragen ruwanta na nan daram har sai an kammala tattaunawa.

Shugaba Trump ya ce akwai yiwuwar tattaunawar sulhu da Iran

A daidai wannan lokaci ana ci gaba da kokarin shirya ganawa ta biyu tsakanin Washington da Teheran bisa shiga tsakanin Pakistan bayan tattaunawar farko da aka yi a karshen makon jiya a birnin Islamabad.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW