Iran: Karuwar sinadarin uranium
November 23, 2022Talla
Tehran ta ce shekaru uku ke nan da suka fara wannan aiki tun bayan da aka wargaza yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 tsakaninta da manyan kasashen duniya.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa IAEA da kasashen yamma ke zargin Iran da mallakar sinadarin da ya wuce kima
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliyar kasar Iran Mohammad Eslami, ya ce matsi da kuma takunkumai ba su ne za su magance matsalar ba.
A karkashin yarjejeniyar da aka cimma a shekarun baya, ba a amince Iran ta sami sinadarin da yawanshi ya kai kaso 4 cikin dari ba wanda ake ganin ya isa duk wata bukata baya ga kera makaman nukiliya.