Iran ta sha alwashi tsatsauran hukunci kan masu boren
January 25, 2026
Kafar yada labaran Mizan ta ruwaito babban jami'in shari'ar Tehran na cewar al'umma sun bukaci a gaggauta yanke hukunci a kan mutanen da suka shirya zanga-zangar, wadanda ake zargi da ta'addanci da tayar da tarzoma.
Sai dai shugaban Amurka Donald Trump wanda ya gargadi mahukuntan Tehran a kan daukar hukunci kisa ta hanyar rataye masu boren inda ya sha alwashin kai hari a kasar muddin ta yi hakan.
Boren da ya samo asali a kan tsadar kayayyakin masarufi da ya rikide ya zuwa na kin jinin gwamnati da kuma kiraye-kiryen murabus din mahukunta, wanda ya zama kalubale babba da jamhuriyar Musulunci ta fuskanta.
A halin yanzu dai, zanga-zangar ta lafa biyo bayan amfani da karfin da ya wuce kima da jami'an tsaro suka yi gami da katsewar intanet, matakan da suka fuskanci kakkausar suka daga kasashen duniya.
Sama da mutane dubu uku ne aka kashe a yayin boren baya ga kame wasu daruruwa.