1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta shirya tsananin hukunci kan masu adawa da gwamnati

January 13, 2026

Rahotannin da ke fitowa daga Iran, na cewa hukumomin kasar za su tsananta hukunci a kan wadanda aka kama da laifin zanga-zangar adawa da gwamnati, wadanda a yanzu suke gaban shari'a.

Shugaba Masoud Pezeshkian na kasar Iran
Shugaba Masoud Pezeshkian na kasar IranHoto: Vahid Salemi/AP Photo/dpa/picture alliance

GWamnatin kasar Iran na tuhumar masu zanga-zangar da ta rikide tare da karade kasar ne da yin fito-na-fito ne da tsari na Ubangiji, laifin kuma da shari'ar Musulunci ke kaiwa ga yanke hukuncin kisa a kansa.

A ranar Litinin ne, babban alkalin kasar ya yi kira a kan hukunci ga masu zanga-zangar da suka kai hari kan ‘yan sanda da sauran wuraren tsaro.

A baya dai lokacin zanga-zangar da aka yi a 2022, akalla mutane 12 aka aiwatarwa da hukuncin kisa bayan zanga-zangar da ta shafi nema wa mata 'yanci.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce sama da mutane 640 sun mutu a zanga-zangar da ta fi girma tun 2022.

Wani jami'in Iran ya ce kimanin mutane 2,000 ne suka mutu tun farkon zanga-zangar makonni biyu da suka gabata.