Iran ta Shirya wani taro a kan Siriya
August 9, 2012A wannan Alhamis,ne kasar Iran ta shirya wani zaman taro a kan batun kasar Siriya inda ta gayyaci kasashen duniya da su taimaka ga kawo karshen zubar da jini a kasar,to saidai kasashen Turai da Majalissar Dinkin Duniya sun ki su amsa kiran. Ministan harakokin wajen kasar ta Iran Ali Akbar Salehi ya ce suna sa ran taron zai cimma wata matsaya ta yadda za'a iya bullo da sabbin dabarun kawo karshen zubar da jini a Siriya. Taron ya hada wasu kasashen Afirka da Asiya da ma na yankin Amirka inda a ke sa ran halartar kasashe kusan 12 zuwa 13. Shugaba Ahamedinejad ya kira kasahen da su yi wani yunkurin kawo tasu gudunmuwa ga samar da zaman lafiya a kasar ta Siriya da ke fama da tashe-tashen hankulla. Kasar ta Iran da ke babbar kawar Siriya na yawan dora alhakin rashin daidaito a Siriya ga kasashe irinsu Amirka ,Saudiya, Qatar da kuma Turkiya.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu