1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Iran ta soki rufe ofishinta na Jakadanci a Jamus

Abdullahi Tanko Bala
November 1, 2024

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bukaci 'yan kasarta su fice daga Iran domin kauce wa yin garkuwa da su. Gargadin ya biyo bayan aiwatar da kisa kan wani Bajamushe dan asalin Iran Jamshid Sharmahd.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi
Ministan harkokin wajen Iran Abbas AraghchiHoto: ATTA KENARE/(AFP

Iran ta ce rufe wasu ofisoshinta na Jakadanci a Jamus da mahukuntan kasar suka yi tamkar takunkumi ne gwamnatin ta kakaba 'yan Iran da ke zaune a Jamus.

Hakan dai na zuwa ne bayan da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock a ranar Alhamis ta sanar da cewa za a rufe ofisoshin jakadancin Iran guda uku da ke Jamus a matakin martani ga kisan wani Bajamushe da ke da asali da Iran Jamshid Sharmahd. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki lamirin matakin a wata kasida da ya wallafa a shafin Internet.

A halin da ake ciki kuma Jamus ta yi kira ga 'yan kasarta da ke Iran su bar kasar tare da yin gargadi ga Jamusawa su kiyayi zuwa kasar Iran.