Iran ta tsare wasu 'yan Burtaniya bisa zargin leken asiri
February 13, 2025
Iran ta tsare wasu 'yan kasar Burtaniya guda biyu bayan zarginsu da aikata laifukan da suka shafi tsaro, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Burtaniya ta sanar ranar Alhamis.
Karin bayani:Iran ta yi allawadai da hare-haren da Amurka da Burtaniya suka kai Yemen
Kafar yada labaran Iran IRNA ta rawaito cewa jakadan Burtaniya a Iran Hugo Shorter ya samu zarafin tozali da mutane biyun da aka kama a lardin Kerman, kuma yana ci gaba da tuntubar hukumomin Tehran a kan batun, to sai dai babu wani karin bayani a kan ganawar.
Karin bayani:Kasashen G7 na shirin kakabawa Iran takunkumi saboda Isra'ila
Iran dai ta yi kaurin suna wajen kama 'yan kasashen waje da tsare su a matsayin fursunonin siyasa, wadanda har yanzu babu alkaluman adadin mutanen da ta cafke, to amma ta yi togaciyar cewa tana kama su ne bisa aikata laifin leken asiri.