1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta yi barazanar martani bayan harin Isra'ila a Beirut

June 7, 2026

Isra'ila ta kai hare-hare a kudancin birnin Beirut na Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sabunta kwanaki kaɗan da suka gabata, lamarin da ya janyo mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu da dama.

Sojojin Iran
Sojojin Iran Hoto: Atta Kenare/AFP

Gwamnatin Isra'ila ta ce ta kai harin ne a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da ƙungiyar Hezbollah ta kai arewacin Isra'ila, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa ƙasarsa za ta ci gaba da matsa lamba har sai ta tabbatar Hezbollah ba ta zama barazana ba.

Sai dai Iran ta yi kakkausar suka kan harin, tana zargin Amurka da bai wa Isra'ila damar ci gaba da kai hare-hare a Lebanon duk da ƙoƙarin sasanta rikicin. Kakakin majalisar dokokin Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya yi gargadin cewa ci gaba da harin da kuma matakan takunkumin Amurka kan Iran na iya sa sansanonin Amurka da kadarorin Isra'ila a yankin su zama halastattun wuraren mayar da martani.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin yarjejeniyar rage tashin hankalin da ke tsakanin Iran, Isra'ila da kuma Hezbollah, duk da cewa rikicin na ci gaba da barazana ga zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW