1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi barazanar sake kulle Mashigin Hormuz

April 18, 2026

Bayan sanar da bude Mashigin Hormuz, Iran ta yi barazanar sake rufe mashigin idan har Amurka ba ta janye takunkumin hana jiragenta wucewa da ta sanya a Gabas ta Tsakiya ba.

Hoto: Shady Alassar/Anadolu Agency/IMAGO

Shugaba Donald Trump ya hakikance kan cewa, takunkumin da Amurka ta sanya kan jiragen Iran na hana su wucewa ta tekun Gabas ta Tsakiya zai ci gaba da kasancewa.  Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce za a garkame mashighin idan har ba a cire takunkumin ba, wanda zai sanya jiragen ruwa sai sun tambayi izinin Iran din kafin su iya wucewa.

Karin bayani:Faransa da Burtaniya na tsara shirin bude mashigin Hormuz 

Shugaba Trump ya kuma yi barazanar cewa zai janye daga yarjejeniyar bude wuta da Iran, idan har ba a cimma yadda za a kawo karshen yaki baki daya ba a ranar Laraba. A gefe guda ya yi ikrarin cewa Iran ta amince da bayar da sinadarinta na Uranium, sai dai kuma Iran din ta musanta hakan.