Iran ta yi fatali da takunkumin Amirka
November 5, 2018Shugaban Iran Hassan Rouhani yace Amirka za ta dandana kudarta tare da yin nadama har abada bisa kakaba mata takunkumin hana safarar danyen mai a kasuwannin duniya.
"Amirka za ta dandana kudarta har abada. Suna zaluntar babbar kasa mai dumbin tarihi da al'da ta gargajiya. Sannan a kullum suna bada hujjoji marasa nagarta. Kasar mu ba za ta lamunci wannan ba. Abun da Amirka ke yi a yau shine kokarin tursasa jama'a da tunzura wasu kasashe. Ba mu kadai muke fushi da Amirka ba hatta kasashen Turai su ma suna adawa da manufofinta."
Amirka dai ta mayar da takunkumin da gwamnatin Obama da manyan kasashe biyar na duniya suka dage a shekarar 2015 game da shirin nukiliyar Iran.
Kasashen Turai wadanda har yanzu suke goyon bayan yarjejeniyar da aka cimma da Iran kan takaita shirinta na nukiliya sun soki lamirin sake kakaba wa Iran din takukmi, yayin da China ta baiyana matakin da cewa abin takaici ne matuka.