1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jana'zar masanin kimiyyar Iran

Zainab Mohammed Abubakar
November 30, 2020

Iran ta gudanar da jana'izar fitaccen masanin kimiyya kuma wanda ya kirkiri shirin nukiliyar sojin kasar, bisa nanata dora alhakin kisan gillar a kan Izra'ila.

Iran Teheran | Beisetzung des getöteten iranischen Atomforschers Mohsen Fachrisadeh
Hoto: Iranian Defense Ministry/Wana News Agency/REUTERS

Sakataren majalisar kolin tsaron kasar Ali Shamkhani, ya yi amfani da wurin jana'izar wajen bayyana yadda Izra'ila ta yi amfani da wasu na'urorin lantarki wajen kashe Mohsen Fakhrizadeh.

A halin da ake ciki yanzu haka dai, ministan tsaron Iran din ya sanar da cewar babu gudu ba ja da baya, dangane da cigaba da aikin da Fakhrizadeh ya fara kafin ya gamu da ajalinsa.

Jana'izar ta samu halartar manyan jami'an gwamnatin Iran da suka hadar da ministan tsaron kasar Amir Hatami da jagoron rundunar juyin juya hali Hossein Salami.