1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi kiran a duba halin da Falasdinawa ke ciki

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 31, 2019

A sakon da ya aikewa taron shugabannin kasashen Musulmi a birnin Makka, Shugaba Hassan Rouhani ya ce ya kamata shugabannin su mayar da hankali kan halin da Falasdinawa ke ciki.

Saudi Arabien Gipfel der arabischen Liga in Mekka
Hoto: Imago Images/ZUMA Press/T. Ganaim

Rouhani ya bayyana hakan ne cikin wata wasika ya wallafa a shafinsa na Internet, inda ya ce bai kamata shugabannin Musulmi su yi watsi da halin da Palasdinu ke ciki ba, a daidai lokacin da Amirka ke ikirarin samar da wani tsari na zaman lafiya Gabas ta Tsakiya da ba ta bayyana ba, wanda ya ce ka iya zama kuskure na wannan karni.

Rouhani wanda ya yi korafi kan rashin gayyatarsa wajen taron, ya bayyana cewa kasarsa a shirye ta ke ta hada hannu da shugabannin Musulmi domin tunkarar abin da ya kira wata "Yarjejeniyar Karni."  Da yake tofa albarkacin bakinsa kan taron na kungiyar kasashen Msuslmi, ministan harkokin kasashen ketare na Iran din Mohammad Javad Zarif ya yi watsi da wasu zarge-zarge da aka ce an yi a taron kan Iran, bayan ayyana Iran din da abokiyar hamayyarta Sauddiya ta yi da cewa ita ce ke zama barazana wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar yankin Gabas ta tsakiya.

Taron shugabannin kasashen musulmi na duniya OIC Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Nabil

Ministan kasashen ketare na saudiyya Ibrahim al-Assaf ya ce tilas kasashen Musulmin su tashi tsaye domin tunkarara Iran. Shi ma a nasa bangaren, sakatare janar na kungiyar ci-gaban yankin Gabas ta Tsakiya, Abdullatif bin Rashid al-Zayani kira ya yi da hada hannu domin daukar tsattsauran matakai kan Iran

"Muna jadda goyon bayanmu ga matakan da Amirka ke dauka kan Iran, da suka hadar da batun nukiliya da yunkurinta na wargaza zaman lafiya da tsaron yankin da goyon bayan da take bai wa 'yan ta'adda da ma goyon bayanta ga kungiyar Hezbollah da dakarun juyin-juya halin Musulunci na Iran din da kuma 'yan tawayen Houthi da ma sauran kungiyoyin 'yan ta'adda."

Sai dai ba duka kasashen da suka halarci taron ne ke marawa wannan kira na Saudiyya da ma kungiyar ci gaban yankin Gabas ta Tsakiyar baya ba, domin kuwa a nasa bangaren shugaban kasar Iraki Barham Salih da ke zama makawabciya ga Iran din ya nunar da kin amincewarsa kan batun.

Shugaban kasar Iran Hassan RouhaniHoto: Reuters/S. Chirikov

"Jamhuriyar Musulumci ta Iran, kasa ce ta Musulmi kuma makwabciya ga Iraki da kashen Larabawa. Magana ta gaskiya ba ma fatan akai wa fannin tsaronta hari, kasancewar mun hada iyaka ta kimanin kilomita 1, 400 baya ga dangantaka da ke tsakaninmu. Hakikanin gaskiya tsaro da zaman lafiyar makabciyarmu kasar Musulmi, na da matukar muhimmanci. Yankin na son tsayuwa da kafafunsa ba tare da shisshigi cikin harkokinsa na cikin gida ba.”

Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya dai ya kira taron ne sakamakon takun sakar baya-bayan nan da ke tsakanin Saudiyya da Iran da kuma Amirka da Iran din a daya bangaren. A wata sanarwa da shugabannin kasashen Larabawan suka fitar yayin taron, sun yi kira ga Iran ta daina abin da suka kira yin shisshigi a yankin, kiran da ma'aikatar harkokin wajen Iran din ta bayyana da maras tushe balle makama.