1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi soki yammacin duniya kan shirin nukiliyarta

September 24, 2012

Shugaban Iran Mahmud Ahmedinijad ya yi kakkausar suka ga ƙasashen yamma dangane da matakin da su ke ɗauka game da shirin ƙasarsa na Nukilya.

ARCHIV - Der iranische Präsident Mahmud Ahmadinedschad bei einer Rede in der Urananreicherungsanlage in Natans (Archivfoto vom 09.04.2007). Der internationale Streit um Irans Atomprogramm schwelt seit Jahren. Die Weltgemeinschaft verdächtigt die Islamische Republik, den Bau von Atomwaffen zu planen. EPA/ABEDIN TAHERKENAREH (zu dpa Hintergrund: "Der Streit um Irans Atomprogramm" vom 11.05.2012) +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaba Ahmedinijad ya yi wannan sukan ne lokacin da ya ke jawabi ga kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a yau inda ya ce ƙasashen da su ka haɗa da Burtaniya da Amurka da Faransa na yin karen tsaye ga 'yancin ƙasashen duniya wanda a cewarsa shi ne ya sanya su ka gaza samo hanya warware rigingimun da ake yi a wasu ƙasashen duniya.

Baya ga wannan, Ahmedinijad ya ce wasu daga cikin ƙasahen da ke da kujerun dindindin a kwamitin sulhun na yin amfani da damar da su ke da ita ba bisa ƙa'ida ba ta hanyar maida wasu ƙasashe 'yan lele wanda a cewarsa hakan ba zai haifawa sauran ƙasashen duniya ɗa mai idanu ba.

daura da wannan bayan jawabi na shugaban Ahmedinijad, babban mai shiga tsakani na Majalisar Ɗinkin Duniya kan rikicin Siriya Lakhdar Brahimi ya ce rikicin da ake a Siriyan tsakanin dakarun da ke biyayya da shugaba Basharul Assad da masu fafutukar kawo sauyi na cigaba da ƙazanta.

Manzon na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce babu alamun rikici tsakanin ɓangarorin biyu zai zo ƙarshe cikin ƙanƙanin lokaci sannan al'ummar da yanzu haka ke zaune a ƙasar baya ga wanda su arce wanda yawansu ya kai miliyan guda da rabi na iya fuskanta ƙarancin abinci kasancewar rikicin bai bari manoma sun gudanar noma ba yadda ya kamata ba.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi