1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da kiran ta kaurace wa ramuwar gayya

Zainab Mohammed Abubakar
August 13, 2024

Wasu kasashen Turai uku sun bukaci Iran da ta kaurace wa duk wani harin ramuwar gayya da zai iya kara ta'azzara rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Hoto: SalamPix/ABACA/picture alliance

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da firaministan Burtaniya Keir Starmer, sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa a jiya Litinin inda suka amince da sabon matakin da masu shiga tsakani watau, Qatar da Masar da Amurka suka yi ganin an cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin Isra'ila da Hamas.

Shugabannin na Turai sun kuma yi kira da a sako dukkan mutanen da Hamas ke garkuwa da su, kana  a bada damar isar da agajin jin kai ba tare da katsewa ba, daura da rokon Iran da kawayenta da su guji kai harin ramuwar gayya da zai iya kara ruruta wutar rikicin yankin, bayan kisan gillar da aka yi wa jagoran siyasar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran,  a karshen watan Yuli.

Bayan shafe fiye da watanni 10 ana gwabza fada, an samu asarar rayukan Falasdinawa kusan duba 40 a Gaza, kamar yadda alkaluman ma'aikatar lafiyar Zirin ke cewa.