1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da daftarin bukatu na tsagaita bude wuta

April 6, 2026

Kasashen Iran da Amurka sun karbi daftarin bukatun tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki 45, daftarin da kasashen Masar da Pakistan da kuma Turkiyya suka gabatar.

Guda daga cikin cibiyoyin makamashin Iran
Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto/picture alliance

A martaninsa, Shugaba Trump na Amurka ya ce daftarin wani babban ci gaba ne, sai dai bai gamsu da shi ba da zai kai ya sanya hannu. Yayin da kamfanin dillacin labaran Iran ya ruwaito ce, gwamnatin Tehran ta yi watsi da bukatar tsagaita wuta, tare da kara jadadda tsayawa kan bakarta na neman a kawo karshen yakin baki daya. Tun da fari daman Iran ta ce ba za ta bude Mashigin Hormuz ba a cikin yarjejeniyar tsagaida wuta ta wucin gadi.

Karin bayani: Amurka ta mika daftarin shirin zaman lafiya ga Iran

Kwarya-kwaryar daftarin na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya ba da sabon wa'adi ga Iran din na bude Mashigin Hormuz zuwa gobe Talata ko kuma ta fuskanci luguden wuta a kan cibiyoyin makamashinta da ma wasu gine-ginen gwamnati.