1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da shawarin Trump na tsagaita wuta

Abdul-raheem Hassan
March 25, 2026

Babbar tashar jiragen sama na Kuwait ya kama da gobara sakamakon harin Iran, bayan da Tehran ta yi watsi da sharudan Amurka na tsagaita bude wuta tare cewa za ta cigaba da yaki har sai an cika mata sharuda.

Iran 2026 | Mojtaba Chamenei wird als neuer Oberster Führer des Iran benannt
Sabon jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba KhameneiHoto: Iran state TV/AP Photo/picture alliance

Gidan talabijin ta kasar Iran a harshen turanci ta rawaito wani jami'in da ba a bayyana sunansa ba, yana cewa "Iran za ta kawo karshen yakin idan ta yanke shawarar yin hakan, idan aka cika mata sharuddan da ta shimfida." ciki har da kawo karshen farmaki a Iran da biyan su diyya da kuma tabbatar mata 'yancin iko da mashigar Hormuz.

Tun da farko wasu jami'ai biyu daga Pakistan, wadanda suka mika shawarwarin Amurka ga Iran, sun bayyana kudurin mai dauke da abubuwa 15, suna masu cewa ta yi magana kan sassauta takunkumi da yin watsi da shirin nukiliyar Iran tare da dena kera makamai masu linzami har da bude mashigin Hormuz.

Bijirewar Iran ya zo ne a daidai lokacin da Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a Teheran, yayin da Amurka ke shirin aika karin dakarun soji zuwa yankin, matakin da Tehran ta ce zai iya kara dagula lamura.