1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta zafafa hare-hare bayan kashe Ali Larijani

March 18, 2026

Iran ta kai hare-haren ne a Isra'ila da kasashen Gabas ta Tsakiya bayan halaka jami'inta Ali Larijani.

Iran ta zafafa hare-hare bayan kashe Ali Larijani
Iran ta zafafa hare-hare bayan kashe Ali LarijaniHoto: Saeed Qaq/Anadolu/picture alliance

Iran ta kaddamar da hare-hare zuwa Isra'ila da wasu ƙasashen yankin Gulf da safiyar Laraba, inda aka ji fashe-fashe a Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar.

Ita ma Saudiyya ta bayar da rahoton cewa ta kakkabe wasu makamai masu linzami da Iran din ta cilla mata.

Iran ta tabbatar da rasuwar shugaban Hukumar tsaronta Ali Larijani

Hare-haren sun zo ne sa’o’i kaɗan bayan kafafen yaɗa labarai na Iran sun tabbatar da cewa sojojin Isra'ila sun kashe Sakataren Majalisar Tsaron kasar, Ali Larijani, a wani harin da suka kai cikin dare.

Haka kuma an kashe Janar Gholam Reza Soleimani, shugaban rundunar Basij ta rundunar juyin juya hali ta IRGC.

Iran ta yi Allah wadai da kisan Soleiman

A wani bangare kuma, harin sama na Isra'ila a tsakiyar Beirut na Lebanon, inda aka rusa wani gini gaba daya.