Jagoran addinin Iran ya zargi Amirka da zagon kasa
January 17, 2020Jagoran juyin-juya halin Musulumci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya yi fatali da duk wata tattaunawa da Amirka da 'yan barandanta a yankin, muddin ba su mutunta al'ummar Iran ba na bin dokokin Islama da kin kaskanci. Wannan dai shi ne karo na farko da Ayatollah Ali Khamenei ke yin jagorancin sallar Jumm'a cikin shekaru takwas da suka gabata, domin kuwa rabonsa da limancin na Jumm'a tun shekara ta 2012.
A wata huduba da ya gabatar da Larabci a karan farko tun shekaru takwas shugaban addinin na Iran ya siffanta harin mai da martanin kan kashe Qasem Soleimani da jiragen Iran suka kai wa sansanin Ainin Asad na dakarun Amirka da ke Iraki a matsayin wata rana daga cikin ranaku masu tsarki da daraja.
Khamenei ya kara da yin fatali da duk wani yunkurin da Amirka ke yi na tankwara kasarsa ta hanyar shirya mata makarkashiya, ciki har da zanga-zangar da ta biyo bayan kakkabo jirgin Ukraine cikin kuskure da dakarun kasar ta Iran suka yi, zang- zangar da ya ce, jami'an liken asirin Amirka sun tsara daga Pentaghon, don kawar da hankalin kasashen duniya dangane da kisan gillar da Amirka suka yi wa Qasem Soleimani.