Fata kan ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran
June 8, 2018Bayan batutuwan taron kolin kungiyar G7 ta kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya da aka fara yau Juma'a a Kanada, batun yarjejeniyar Iran zai kasance lamari bai sarkakiya musamman barazanar takunkumin da Amirka ta yi na sanyaya gwiwa na kamfanoni daga bangarorin duniya tare da tara mai yawa ga duk wanda ya yi huldar kasuwanci da Iran.
Alamu dai sun nuna takunkumin zai yi tasiri a kan kamfanonin Turai da ke hulda a cikin Iran wadanda suka hada da kamfanin mai Total na Faransa da kamfanin motoci na Faransa wato PSA.
A waje guda dai manyan kasashe uku na Turai da suka hada da Jamus da Faransa da Birtaniya tare da kungiyar tarayyar Turai sun nuna adawarsu da yunkurin hana kamfanonin Turan yin hulda da Iran.
Yayin da ake wannan dambarwa ta diflomasiyya, ganawar bayan fage da Shugaba Rouhani da zai yi da Shugaban Xi Jingping na China daura da taron kolin abu ne da ya dauka da matukar muhimmanci da kuma ganawa da Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Kawo yanzu dai babu daya daga cikin kasashen China da Rasha da ta amince da burin da Amirka take so ta cimma na shake makogwaron tattalin arzikin Iran domin kawo sauyin gwamnati a kasar.