Iran tana shirye da duk wani hariin Amurka
May 20, 2026
Gwamnatin Iran ta ce tana shirye da fuskantar sabbin hare-hare soja yayin da ake kara samun zaman tankiya tsakanin kasar da Amurka. Shugaban majalisar dokokin kasar Mohammed Bagher Ghalibaf ya ce suna sane da cewa abokan gaba na shirin fara sabon yaki.
Ci gaba da neman sulhu
Wannan na zuwa bayan ziyarar ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsin Naqvi zuwa birnin Tehran na Iran inda ya gana wakilan kasar Iran kan zagaye na biyu na tattaunawa. Ita dai Pakistan ta shiga gaba wajen ganin an cimma matsaya ta hanyar tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, inda ta karbi bakuncin zagaye na farko na tattaunawar.
Tun watan Afrilun aka tsagaita wuta a yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kasar ta Iran, a karshen watan Febrairun wannan shekara ta 2026.