Iran tayi na´am da tayin Amurka
October 7, 2007Talla
Iran tayi na´am da tayin shugaba Bush na tattaunawa kai tsaye a game da shirin ta na mallakar makamin Atom. To sai kuma Iran din tace zata yi hakan ne, ba tare da dakatar da shirin ta na sarrafa sanadarin Uranium ba. Kalaman na Iran sunzo ne kasa da mako daya bayan, shugaba George Bush yace Amurka a shirye take ta tattauna da Iran din. Mr Bush yace Amurkan zata tattauna da Iran din ne kawai, idan kasar tayi watsi da aniyarta na mallakar makamin na atom. Kafafen yada labarai sun rawaito kakakin gwamnatin na Iran Mohd Ali Hossein na cewa, iran a shirye take ta shiga tattaunar, amma ba tare da Amurka ta gindaya mata wasu sharruda ba.