Iran: Wata 'yar jarida za ta yi zaman kaso
December 1, 2018Talla
Baya ga shekaru 12 da Hengameh din za ta shafe a tsare, kotu har wa yau ta haramta mata shiga harkoki da suka danganci siyasa da shiga kungiyoyin fafutuka da kuma yin ita kanta fafutukar a kafafen sadarwa na zamani. Da dama dai na alakanta wannan dauri da aka yi mata da irin caccakar bangaren shariar kasar da ta rika yi a shekarun baya, a lokacin da kotunan kasar suka rika daure 'yan jarida da masu fafutuka.