1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran za ta kai hari sansanonin Amurka na Gabas ta Tsakiya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 7, 2026

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce harin bai zama farmaki ga kasashen Gabas ta Tsakiya ba, face Amurka.

Mininstan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi yayin ganawarsa da takwaransa na Oman  Badr bin Hamad bin Hamood Albusaidi a birnin Musqat
Mininstan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi yayin ganawarsa da takwaransa na Oman Badr bin Hamad bin Hamood Albusaidi a birnin MusqatHoto: Issa Iraisi/Xinhua/picture alliance

Iran ta sha alwashin kai hari kan sansanonin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya, matukar ta kuskura ta kai ma ta hari, kuma kada kasashen yankin su dauki cewa su ta kai wa hari, face Amurka.

A tattaunawarsa gidan talabijin na Al Jazeera ranar Asabar, kwana guda bayan kammala tattaunawar zangon farko tsakanin Tehran da Washington, a birnin Musqat na kasar Oman, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, ya shaida cewa kofarsu a bude take, don ci gaba da tattaunawar, ko da ya ke ba a kai ga tsayar da rana ba.

Karin bayani : Shugaba Trump ya ce Iran ta kagu ta cimma sulhu da Amurka

Tuni aka jiyo shugaba Donald Trump na Amurka na cewa a farkon mako mai kama ne za su ci gaba da tattaunawa da Iran, kan batun kwance damararta ta kera makamin nukiliya da ma sauran batutuwan tsaro.