1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Amurka ta fanshi fursunoninta da Iran ta tsare

September 18, 2023

Amurka ta tura wa Iran wasu kudadenta da ta kame a matsayin kudin fansar fursunoninta da Teheran ke tsare da su.

Iran za ta saki fursonin Amurka bisa biyan fansaHoto: K. Steinkamp/blickwinkel/McPHOTO/picture alliance

Kimanin dala biliyan shida ne Amurka ta bura wa Iran ta hanyar bankunan Qatar, a wani mataki na share fagen musayar fursunoni da kasashen biyu za su yi.

Karin bayani: Takaddama kan kudaden Iran da Amurka ta rike

Majiyoyi da dama sun ce tuni wani jirgin saman Qatar ya isa Teheran babban birnin Iran, da nufin jigilar fursunonin biyar dukanninsu Amurkawa da kuma wasu 'yan uwansu guda biyu. Daga cikin fursunonin har da hamshakin mai kudin nan Siamak Namazi, wanda hukumomin Iran suka tsere tun a shekarar 2015 bayan da kotun ta yanke masa hukuncin dauri na shekaru 10 bisa zarginsa da aikata laifin leken asiri.

Karin bayani:Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutum uku 

Wannan musayar fusnoni na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Iran Ebrahim Raissi ke shirin isa birnin New York na Amurka inda zai halarci taron koli na Majalisar Dinkin Duniya