1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran za ta yi afuwa ga fursunoni

April 30, 2022

Albarkacin watan azumin Ramadana da ake shirin kammalawa, kotun koli a Iran za ta yi afuwa ko kuma rage wa'adin zaman gidan kaso ga fursunoni fiye da dubu 1,500.

Ayatollah Ali Khamenei
Hoto: IRANIAN LEADER PRESS OFFICE/AA/picture alliance

Shugaban kotun Ayatollah Ali Khamenei ya ce za a yi afuwar ne a matsayin barka da Karamar Sallah ga al'ummar musulumai ke dab da gudanar da bukukuwanta. 

Shugaban kotun Kolin tare da hadin gwiwar shugaban bangaren shari'a na Iran kan yi afuwa ga dimbin fursunoni a lokutan bukukuwan addinin musulunci.

Ana san ran gudanar da bikin sallah karama ta bana a Iran a ranar Litinin mai zuwa.