Al'ummar Iran na zaben 'yan majalisar dokoki
February 26, 2016Talla
Al'ummar kasar Iran sun fita tashoshin kada kuri'a dan zaben mambobi na majalisar dokokin kasar 290 da ma majalisar kwararrun malamai mai mambobi 88 wadanda ke zabe ko ma su saukar da shugaban addini da ke zama kololuwa a kasar, tuni shugaban addini na kasar Ayatollah Khamenei ya kada kuri'arsa a wannan zabe.
Zaben da ke zama na farko tun bayan da kasar ta warware rikicinta da kasashen duniya kan batun shirinta na makamin nukiliya.
An dai bude tashoshin kada kuri'a 53,000 a fadin kasar yayin da mutane miliyan 55 'yan kasar ta Iran ke zama wadanda suka cancanci kada kuri'a.