1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar takunkumin Amirka kan Iran

Mohammad Nasiru Awal
April 24, 2019

Daga ranar 2 ga watan Mayu wa'adin sassauci da Amirka ta yiwa wasu kasashe takwas kan sayen man Iran ke karewa. Shin hakan na nufin za a shiga wani mummunan yanayi ke nan? 

Bildkombo Donald Trump und Ali Khamenei
Hoto: Imago/UPI//Imago/Russian Look

A bara kasar Amirka ta yi gaban kanta inda ta dora wa kasar Iran sabbin takunkumai. Sai dai ta tsame wasu manyan kasashe takwas da suka fi sayen man fetur din Iran daga takunkuman. Daga ranar 2 ga watan Mayu mai kamawa wannan wa'adi na sassauci ke karewa. Bisa matakin na Amirka dai kasashe irin su China da Indiya da Koriya ta Kudu da Turkiyya da Italiya da Japan da Girika da Taiwan ba su iya sayen man fetur daga Iran ba. Shin hakan na nufin za a shiga wani mummunan yanayi ke nan? 

Matatar mai ta Asalouyeh a kasar IranHoto: picture-alliance/AP Photo/V. Salemi

Bayan sanarwar da Amirka ta bayar cewa ba za ta sabunta wannan wa'adi ba, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi  da ba a ga irinsa ba tun a watan Nuwamban bara. A ranar Talata farashin gangar man ya kusan dalar Amirka 75. Farashin na iya haura dala 80 idan aka aiwatar da matakin sau da kafa a cewar Eugen Weinberg mai nazari kan harkar danyun kaya na Kommerzbank a Jamus.
"Da ma dai akwai karancin man fetur da ya kai na ganga dubu 500 a rana a kasuwar hada-hadar man fetur sakamakon rage yawan mai da kungiyar kasashe masu arzikin mai wato OPEC ta yi. Idan aka kawo karshen wannan wa'adi na sassauci kan kasashen takwas to gibin zai kai na ganga miliyan biyu a rana. Saboda haka ba za a iya kawar da yiwuwar tashin farashin mai fiye da dala 80 a kowace ganga ba."

Wasu sojin kundunbala na AmirkaHoto: imago/ZUMA Press/D. Morgan

Masanin ya kara da cewa ana kyautata fata kasashe kamar China ko Indiya za a iya sabunta musu wa'adin ko kuma su ki shiga cikin takunkuman. Ma'akaitar harkokin wajen China wadda ke kan gaba wajen sayen man fetur daga Iran, ta soki takunkuman Amirka da kakkausan lafazi tana mai cewa harkar kasuwanci tsakanin Iran da sauran kasashen ana tafiyar da ita bisa doka yayin da takunkuman da Amirka ta sanya ba sa kan doka, saboda haka ta yi kira ga Amirka da ta nuna halin ya kamata. 
Ita kuwa kasar Indiya da ke sahu na biyu a jerin kasashen da suka fi sayen fetur daga Iran, tana duba hanyoyin sayen wannan haja daga wata kasa. Su kuma a nasu bangare kasashen Turai sun kafa wata kungiya da za ta tafiyar da harkar kasuwanci da Iran duk da takunkuman na Amirka. Kawo karshen wa'adin sassaucin ya nuna yadda masu matsanancin ra'ayi da ke cikin gwamnatin Amirka suka samu galala inji Sascha Lohman na cibiyar kimiyya da siyasa da ke birnin Berlin.

"Matakin kara matsa lamba da Amirka ke dauka na nufin za a kara yawan takunkuman. A lokaci guda kuma ana kara yi wa Iran barazana. Yanzu haka an girke jiragen ruwa biyu masu daukar jiragen saman yaki a tekun Bahar Rum da nufin tsananta barazanar da za ta kai ga daukar matakan soji. Wannan alama ce ta tabarbarewar halin da ake ciki."

Ministan albarkatun man fetur na Iran Bijan Namdar Zanganeh ya ce Amirka ba za ta samu nasara a matakan na hana Iran fid da man ketare ba. Abin da ake son gani a aikace shi ne ko za a samu masalaha bayan ranar 2 ga watan Mayu ta yadda gwamnatin Iran za ta ci gaba da sayar da manta tsakanin ganga miliyan daya zuwa miliyan daya da rabi a rana, kasancewa tattalin na matukar bukatar kudaden. Ga Amirka ma dai akwai kasada domin babu tabbas ko kasar Saudiyya za ta iya kara yawan man da take hakowa nan-take don cike gibin da za a samu.