IS ta dauki alhakin harin Manchester
May 23, 2017Kungiyar IS ta dauki alhakin harin ta'addancin da aka kai cibiyar raye-raye na birnin Manchester da ke yammacin Ingila, inda mutane 22 suka mutu yayin da 59 kuma suka jikata. Cikin wata sanarwa da ta watsa da kafofin sadarwa na zamani IS ta yi barazanar dasa wasu nakiyoyin.
Rundunar 'yan sandan Birtaniya ta ce wanda ya kai harin ya rasa ransa bayan da ya tada bam da ke daure a jikinsa. Sannan kuma ta bayyana cewar ta kama wani matashi mai shekaru 23 da haihuwa bisa zarginsa da marar hannu a wannan harin, wanda ya zo watanni biyu bayan na London da ya salwantar da rayukansu mutane biyar.
sarauniya Elisabeth ta Ingila ta mika jajenta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin na Manchester. Yayin da Firaminista Theresa May ta yi tir da wannan harin.