IS ta dauki alhakin hannu a harin da ya hallaka mutum 63
August 18, 2019Talla
Kungiyar ta wallafa a wani shafinta na yanar gizo, yadda ta aika da wata mata da aka yi wa damara da bama-bamai, dakin da jama'a ke shagalin bikin auren. Kafin jama'a su ankara, bama-baman sun tarwatse. Shugaban kasar Ashraf Ghani, ya yi tir da alla-wadai da harin, ya kuma baiyana takaici kan rashin shigar da bangaren gwamnati a tattaunawar sulhu da Amirka da kuma kungiyar Taliban ke yi da ya ce, wani babban nakassu ne ga shirin samar da dawamamiyar zaman lafiya a kasar.
Duk da cewa, IS ta yi kaurin suna a kai wa kasar hare-haren ta'addanci, wannan harin da ya rutsa da mata da yara kanana, ya girgiza kasar dama sauran kasashen duniya da ke yi wa kasar fatan samun zaman lafiya.