IS ta daukin alhakin hari a Masar
December 29, 2017Talla
Tsagerun kungiyar IS masu kaifin kishin addinin Islama sun dauki nauyin alhakin harin da aka kai kan wata majami'a da ke wajen birnin Alkahira na Masar. Wani dan bindiga dadi da ya hallaka mutane 10 lokacin da ya bude wuta a majami'ar da ke wajen birnin na Alkahira. Wani dan sanda ya harbe dan bindigar har lahira bayan kai harin. Sannan an kama mahari na biyu.
Rahotanni sun nuna cewa dan sanda daya na daga cikin wadanda aka hallaka, akwai kuma wasu jami'an tsaro takwas wadanda suka samu raunika. Kasar ta Masar ta gamu da hare-haren tsagerun kungiyar IS masu kaifin kishin Islama lamarin da ya kai ga mutane mutane da dama. Kiristoci sun kunshi kashi 10 cikin 100 mutanen mutanen kasar ta Masar kimanin milyan 93.