Mayakan Kungiyar IS sun kai hari kan fararen hula
February 18, 2023![](https://static.dw.com/image/64748708_800.webp)
Talla
Kafafofin yada labarai na kasar Siriya sun tabbatar da mutuwar mutum akalla 68 da suka ce sun mutu ne a sakamakon wani harin kwanton bauna da ake zargin mayakan IS da kai wa. Fararen hula 61 da suka kasance mafarauta da kuma sojoji bakwai ne suka gamu da ajalinsu a sakamakon harin.
Harin na birnin Homs a daren Jumma'ar da ta gabata, ya kasance hari mafi muni da mayakan ke kai wa yankin Homs a fiye da shekara guda a kasar da rikici ya daidaita. Kawo yanzu babu wata sanarwa daga bangaren mayakan na IS da ba sa wata-wata wajen sanar da daukar alhakin kai hare-harensu.