IS ta yi barna mai yawa a Siriya
December 18, 2014Talla
Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya ta tabbatar da cewa 'yan uwan mutanen da aka kashe din ne suka gano gawarwakin a wani katon kabari a gundumar Deir Ezzor, wanda hakan ya kawo yawan 'yan kabilar Shaitat da 'yan IS din suka kashe a gundumar ta Deir Ezzor da ke kusa da kasar Iraqi zuwa sama da 900. Kungiyar kare hakkin dan Adam din da ke da Shalkwata a Birtaniya ta ce mafiya yawan wadanda aka kashe a yayin da kungiyar ta IS ta kai farmaki a gundumar, fararen hula ne da suka tashi tsaye suka nuna adawa da kungiyar.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu