Kungiyar IS ta wallafa bidiyon kisan mutane a Najeriya
December 27, 2019![Boko Haram Flagge (S. Yas/AFP(Getty Images)](https://static.dw.com/image/18241332_800.webp)
Talla
Faifan bidiyon da aka wallafa a shafukan kungiyar na farfaganda Amaq ya nuna mutanen daukacinsu an rufe fuskokinsu, inda aka bindige na farko kan daga bisani a yayyanka naman sauran jama'ar da kungiyar ta yi garkuwa da su.
A gabanin yanka jama'ar daya daga cikin 'yan kungiyar ya gabatar da jawabinsa inda ya nuna kisan mutanen a matsayin wani sako ne ga mabiya addinin Kirista, kana kuma kisan na a matayin wata ramuwar gayya ce domin daukar fansan kisan jagoran kungiyar ta IS Abou Bakr Al-Bagdhdadi, wanda sojojin Amirka suka yiwa dirar mikiya a cikin watan Oktoban da ya gabata a wata mabuyarsa da ke kasar Siriya.