1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isaac Herzog na ziyara a Hadaddiyar Daular Larabawa

Abdourahamane Hassane
January 30, 2022

Wannnan ziyara ita ce ta farko da wani shugaban Isra'ilan yake kai wa a wata kasar Larabawa da ke cikin yankin Gulf,

Abu Dhabi Israel Präsident Herzog Staatsbesuch
Hoto: Amos Ben-Gershom/Government Press Office/REUTERS

Shugaban kasar Israila Isaac Herzog na yin ziyara a Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannnan ziyara ita ce ta farko da wani shugaban Isra'ilan yake kai wa a wata kasar Larabawa da ke cikin yankin Gulf, tun bayan da kasashen biyu suka sake farfado da hulda a shekara ta 2020. Shugaban na Isra'ila zai gana da ministan harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawa Abdallah Ben Zayed kafin ya isa a Dubai inda zai gana da shugaban gwamnatin domin tattauna wasu batutuwan masu mahimmanci. Kasashen Baharen da Hadaddiyar Daular Larabawa su ne kasashe na farko da suka sake dawo da hulda da Israila tun a shekarun biyun da suka wuce.