ISIS ta kafa shari'ar musulunci a Mosul
June 25, 2014Jami'an Kungiyar ta ISIS sun yi ta tsala wa wani dattijo da ya aurar da 'yarsa cikin iddar saki bulala har guda hamsin, bayan da alkalin da ya yanke hukuncin ya ce shi ne mafi sassauci a tsarin na shari'a. Ya ce "Na yanke hukuncin bulala 50 kan wannan dattijo, shi kuwa wanann saurayi bulala 40, saboda aurar mata da yayi cikin iddar saki, bayan da ya yi fatali da gargadin da akai masa na haramcin yin aure cikin idda"
Shi kuwa wani dattijo da ya kawo karar wani Amiri da kungiyar ta wakilta a unguwanni, kan zaluntarsa da ya ce amirin ya yi, yaba wa tsarin shari'ar da 'yan Kungiyar ta ISIS ke aiwatarwa ya yi. Ya ce "Muna yi wa Allah godiya kan wannan shari'ar da ba ta nuna banbanci tsakanin 'yan kasa. Na kawo karar wani Amiri, amma yanzu har an yanke masa hukuncin dauri.Daular musulunci mai tabbatar da adalci ita ce ke da ikon daukacin wannan jihar."
Wasu na adawa da shari'ar musulunci a Iraki
A daura da haka, mutane da dama a garin na Mosul na kokawa da tsauraran dokokin da kungiyar ta ISIS suka gindaya, kama daga hana aske gemu da dangale wando gami da rufe gidajen sinima da kuma hana mata sanya wanduna ko yawo ba dankwali, kamar yadda suka hana sayar da taba. Lamarin da ya kai aka fara sayar da ita a boye. Wani matashi da ya fasa wani shago don ya saci taba sigari da ya matsu da shanta amma bai samu ba, kutun ce ta yanke masa hukuncin datse hannu da aka zartar da shi nan take.
Akeel Shahata, wani malami a garin na Musil ya ce matakin da 'yan ISIS ke dauka, hada karya ne da gaskiya. Ya ce "Bai halarta ga wani musulmi ya zuba da jinin dan uwansa da sunan haddi ba. Su ma wadanda shari'ar ta lamunce musu, ba za su yi hakan ba har sai an samu tabbatar da tsarin adalci na musulunci da zai ba wa kowa hakkinsa na rayuwa cikin mutunci. Idan aka bar shari'a haka kara zube, duk wata kungiyar tsagerun da ta ke rike da makamai, za ta yi ta kashe musulmi da sunan sun saba mata ko sun yi ridda."
Bugu da kari,masu kaifin kishin Islaman na ISIS sun ruguza daukacin mutum- mutumin tarihi 3 dake birnin na Mosul, kama daga mutum-mutumin Sayyada Maryama, mahaifiyar Annabi Isa A.S, da na wani shaharren mawaki kuma marubucin adabi, Abu Tammam, da kuma na wani dan kishin kasa, Mulla Usman. Suna daukar mutum-mutumin a matsayin gumakan da ake bautawa.
Mawallafi: Mahmud Yaya Azare daga Alkahira
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe.