Isra'ila: Amincewa da sabon kudin shari'a
July 24, 2023Firaministan Izra'ila Benjamin Netanyahu ya sake mika wa majalisar dokokin kasar kudin shari'ar da ya kudri aniyar yi wa wa gyaran fuska domin yin kuri'ar amince wa ko kuma watsi da shi.
Sai dai gabanin kuri'ar, shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci da a dage ranar zuwa gaba, la'akari da sabanin ra'ayoyi daga bangarorin siyasan kasar wanda ya haifar da boren da aka share dogon lokaci ana yi don kalubalantar shirin.
Kazalika ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, yayin wata hira da ta yi da takwaranta na Izra'ila ta nuna mahinmanci ba wa fannin shari'a cikekkyan iko tare kuma da kira da a jinkirta kuri'ar da za kada a yau.
Masu adawa da wannan shirin dai na alankanshi da yi wa dimokuradiyya karan tsaye, duba da wasu tanade-tanaden da sabon kundin ya yi wandanda ke ba wa gwamnatin karfin iko fiye da ma'akatar shari'a.
A daya gefen kuma, wasu masana na yi wa shirin na mista Netanyahu, kallon matakin da ka iya ba shi kariya kan wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.