1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Isra'ila: An kai hari ofishin jakadancin ta a Indiya

December 26, 2023

Jami'an 'yan sanda a birnin New Delhi na Indiya na ci gaba da gudanar da bincike kan wani bam da ya tashi a kusa da ofishin jakadancin Israila.

Hoto: Danish Siddiqui/REUTERS

Jami'an 'yan sanda a birnin New Delhi na Indiya na ci gaba da gudanar da bincike kan wani bam da ya tashi a kusa da ofishin jakadancin Israila.

'Yan sandan dai sun yi wa ofishin kawanya domin gano wadanda suke da hannu a tashin bam din, duk da cewa babu rahotannin asarar rayuka ko kuma jikkata.

Ohad Nakash Kaynar, mataimakin babban jami'in diflomasiyyar Isra'ila a New Delhi, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bada tabbacin cewa dukkan ma'aikatan ofishin  diflomasiyyar da sauran ma'aikata suna cikin koshin lafiya, kuma jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike.

Wani jami'in tsaro da ke aiki a rukunin ofisoshin diflomasiyyar da ke da cikkakken tsaro, ya ce ya ji karar bam din, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran India Press Trust.