1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici a zirin Gaza

Zulaiha Abubakar
November 15, 2019

Sojojin kasar Isra'ila sun sanar da kai wa mayakan Jihadil Islam da ke zirin Gaza sabon hari, kwana guda bayan amincewa da tsagaita wuta a ci-gaba da shirin kawo karshen yakin da ya dauki shekaru ana fafatawa.

Gaza Israel Raketenabwehrsystem Iron Dome
Hoto: Reuters/A. Cohen

Sanarwar ta kara da dora alhakin karya wannan yarjejeniya kan mayakan na Jihadil Islam, wadanda suka harba wa fararen hular Isra'ila makami da misalin karfe 05:30 na asubahin wannan Jumma'a daga zirin na Gaza.

Gabanin kulla yarjejeniyar tsagaita wutar, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a rikicin yankin Gabas ta Tsakiya Nickolay Mladenov ya roki bangarorin biyu da su yi kokarin yin hakuri da juna don a samu wanzuwar lafiya a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter, rokon da a yanzu yankunan biyu suka yi watsi da shi.