Isra'ila ba ta neman kujera a kwamitin MDD
May 5, 2018Talla
Isra'ila dai na cikin jerin kasashe uku da ke muradin kaiwa ga kujeru biyu a wannan kwamiti mai karfin fada a ji a Majalisar Dinkin Duniya daga watan Janairu. Sauran kasashen kuwa su ne Jamus da Beljiyam.
Kwamitin Sulhun dai na da mambobi biyar na din-din-din wato Amirka da Rasha da China da Birtaniya da Faransa sannan mambobi goma da ake zaba bayan kada kuri'ar mambobi 193 inda su kan yi wa'adin karba karba na shekaru biyu-biyu. Janyewar ta Isra'ila dai ta ba wa Jamus da Beljiyam tabbacin samun kujerun biyu a zaben da za a yi a ranar 8 ga watan Yuni.