Isra'ila da Falasɗinawan Gaza na ci gaba da kai wa juna hari
August 25, 2014Aƙalla Falasɗinawa biyar aka kashe a Gaza yayin da Isra'ila ke ƙara kai farmaki ta sama a kan waɗanda ta kira 'yan ta'adda a Zirin Gaza. Shaidu sun ce wani hari ta sama ya lalata wasu gidaje huɗu a garin Beit Lahiya, da ke kusa da kan iyakar Zirin Gaza da Isra'ila, garin kuma da Isra'ila ta ce ya zama dandalin harba rokoki cikin ƙasar. Kungiyar Hamas da ke iko a Zirin Gaza ta ce ba za ta daina faɗa ba har sai an janye killacewar da Isra'ila da kuma Masar suka yi wa mazauna Zirin Gaza su kimanin mutum miliyan 1.8. Sami Abu Zuhri shi ne kakakin Hamas ya ce duk da ƙoƙari tare da kiraye-kirayen na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, amma "har yanzu ba bu komai a kasa."
Ya ce za su ci gaba da gwagwarmayar kare al'ummar Falasɗinu daga wannan cin zali na Isra'ila, "har sai an biya bukatun Falasdinawa."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane