1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila da Falasɗinu na shirin takun saƙa a Majalisar Ɗinkin Duniya

September 16, 2011

Yayin da Falasdinawa ke shirin gabatar da buƙatar kafa 'yantacciyar ƙasarsu, Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya buƙaci Falasɗinawan da kuma Isra'ila su nuna halin dattako.

Shugaban Hukumar Palesdinu Mahmud AbbasHoto: picture alliance/dpa

Falasɗinawa na cigaba da matsa kaimi ta neman amincewar Majalisar Ɗinkin Duniya domin kafa 'yantacciyar su. Ministan harkokin wajen Falasɗinawa Riyad al-Malik ya shaidawa 'yan jarida cewa za su gabatar da buƙatarsu ga kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya duk kuwa da cewa Amirka ta yi alƙawarin hawa kujerar naƙi idan batun ya taso. Jami'an diplomasiyar Amirkan sun yi ta kai gwauro suna kai mari domin shawo kan Falasɗinawan su jingine wannan buƙata inda sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta yi bayani da cewa " hanya ɗaya tilo ta samun dawwamammiyar masalaha, ita ce ta tattaunawa kai tsaye a tsakanin ɓangarorin kuma tafarkin samun hakan ya dogara ne ga birnin ƙudus da kuma Ramallah amma a birnin New York ba".

Bisa ga dukkan alamu dai za'a yi takun saƙa tsakanin shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas wanda zai gabatar da buƙatar kafa ƙasar ta Falasdinu da kuma Firaministan Israila Benjamin Netanyahu wanda yace shima zai gabatar da jawabi ga Majalisar Ɗinkin Duniyar tare da zayyana hujjojin su na ƙin amincewa da 'yantacciyar ƙasar Falasdinawa. A waje guda dai sakataren Majalisar Ɗinikin Duniya Ban Ki-Moon ya yi kira ga ɓangarorin biyu da su nuna halin dattako

" Yace ina kira a garesu da su shiga tattaunawa mai ma'ana, gamaiyar ƙasa da ƙasa na da haƙƙin samar da kyakyawan yanayi da ya dace da wannan, hakan kuwa na nufin Israila tana da haƙƙin samar da wannan yanayi, batun gina sabbin matsugunan yahudawa ko kaɗan bai taimaka ba, a waje guda kuma suma Falasɗinawa ya kamata su duba batun tattaunawa da Israila, Ina tausayawa halin ƙunci da Falasɗinawan ke ciki waɗanda burin su na samun 'yantacciyar ƙasa musamman ƙarƙashin tsarin ƙasashe biyu da za su zauna daura da juna cikin girma da arziki har yanzu bai wakana ba."

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita Yahouza Sadissou Madobi