Isra'ila da Falasɗinu sun hau teburin sulhu
March 18, 2012Hukumomin Isra'ila dana Falasɗinu suna gudanar da tattaunawar da ta shafi tattalin arziƙi a tsakanin su duk kuwa da jinginar da tattaunawa da ta shafi zaman lafiya, a wani matakin sake warware batun harajin Falasɗinu da Isra'ila ke karɓa a madadin hukumar Falasɗinawa gabannin ta miƙa mata. Jami'an da suka sanar da hakan sun ƙara da cewar matakin zai taimakawa gwamnatin Falasɗinu shawo kan matsalar bashin dake kanta. Tun bayan da Isra'ila ta mamaye gaɓar tekun Jordan a shekara ta 1967 ne sassan biyu suka cimma wata yarjejeniyar wucin gadin da ta tanadi Isra'ila ta karɓi harajin daya shafi harkokin Kwastam a madadin Falasɗinu, wanda kuma ya kai na kuɗi dalar Amirka miliyan 100 a kowane wata akan kayayyakin da aka shigo da su daga yankunan.
Sai dai kuma Isra'ila ta dakatar da miƙawa Falasɗinu harajin nata a lokacin da sassan biyu suka fuskanci taƙaddamar diflomasiyya da kuma na tsaro, abinda kuma ya janyo Allah wadai daga ƙasashen duniya daban daban. A tsokacin daya yi game da taron, ministan kuɗin Isra'ila Yuval Steinitz ya shaidawa maneman labarai cewar, ko da shike lamarin na da matuƙar wahala, amma yana fatan taron zai cimma nasara domin amfanar sassan biyu, wato Isra'la da Falasɗinu.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar