1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar Oslo ta gaza samar da zaman lafiya

Usman Shehu Usman HD
September 13, 2018

Shekaru 25 bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Falasdinawa da Isra'ila, yarjenjeniyar da aka sani da "Kudurin Oslo", wacce aka amince a samar da kasashe biyu da ke makotan juna tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

USA Weißes Haus Unterzeichnung von Oslo 1  Präsident Bill Clinton (M) Israels Premierminister Yitzhak Rabin und PLO Vorsitzender Jassir Arafat
Hoto: picture-alliance/CPA Media

Shugaban Falasdinawa Yasser Arafat na wancan lokacin da marigayi Firaminista Yitzhak Rabin na Isra'ila, su ne suka sa hannu kan yarjejeniyar karkashin sa idon tsohon Shugaban Amirka Bill Clinton. Yarjejeniyar zaman lafiyan da aka cimma, ga wadanda suka taka rawa aka samu tattabar da ita, suna cewa inda an aiwatar da ita kawo yanzu da an kawo karshen zubar da jini a yankin. Ga al'ummar kasar ta Norway kuwa har yanzu suna alfahari da wannan rawar da kasarsu ta taka a wancan lokacin, inda har ta kai ga amincewa da yarjejeniya kan rikici mafi sarkakiya a duniya.

A wancan lokacin dai an amince da cewar Isra'ila da Falasdinawa za su yi aiki tare don bai wa Falasdinawa 'yancinsu, a bisa abin da Majalisar Dinkin Duniya ta yarda, wato gabashin Kudus ya kasance babban birnin Falasdinawa, yayin da za a shata kan iyakar kasashen biyu.

Ba a dai fasa fafatawa ba tsakanin Falasdinawan da sojan Isra'ilaHoto: Reuters/I. Abu Mustafa

Kafin wannan lokacin dai hukumomin Isra'ila sun dauki shugaban Falasdinawa a matsayin dan ta'adda.

Sai dai sannu a hankali wannan yarjejeniyar ta ruguje, musamman bayan da aka hallaka Firaminista Yitzhak Rabin na Isra'ila wanda ya sa hannu kan yarjejeniyar. A yanzu wannan yarjejeniyar ta Oslo ta zama sai dai a takarda, domin Isra'ila sai kara ba da dokar rusa kauyukan Falasdinawa take yi, inda kuma ita kanta kasar Amirka mai shiga tsakani, a karshin gwamnatin Trump ta fito a fili ta nuna cewa ita ta dauki bangarei, kuma har ta hana kudin tallafin da ake ba wa Falasdinawa, ta dawo da ofishin jakadancinta Birnin Kudus, kuma ta kori wakilan Falasdinawa a kasar Amirka. Baya-bayan nan Donald Trump ya ce kawai a hade yankin Falasdinawa da Jordan su zama kasa daya.