Isra'ila ta yarda da yarjejeniyar tsagaita wuta
May 21, 2021Talla
Rahotannin na cewa kasar Masar da ta shiga tsakani, zata tura da wakilai biyu zuwa Tel Aviv da kuma yankunan Falasdinawa don ganin yadda ake aiwatar da yarjejeniyar.
Tuni dai Faladinawa suka kaure da murna biyo bayan fara aikin tsagaita wutar, tare da daga tutoci da kuma harbi a iska a zirin Gaza. Bangarorin biyu dake rikici dai sun baiyana tsagaita wutar a matsayin nasara.