Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita wuta
November 22, 2012Daga daren ranar Talata izuwa yammacin ranar Laraba, Isra'ila ta yi ruwan rokoki a yankin Gaza fiye da guda 40 akan wasu gine ginen gwamnatin inda mutane a ƙalla guda 26 suka rasa rayukansu.Baya ga wata rokar da ta faɗa akan wani Hotel wanda a cikin sa yan' jaridu na ƙasashen duniya ke da masabki, sai dai babu wanda ya samu rauni:Ko da shi ƙarfi ba ɗaya ba amma da alama al'umma Isira'ila na tattare da zulumi da fargaba dangane a yadda ƙungiyar Hamas ɗin ita ma ke harba rokoki .kuma a hari na baya baya nan da ya auku a yau a birnin Ƙudus wani abu ya fashe a cikin wata motar bus inda mutane da dama suka jikata.
Yunƙurin ƙasashen duniya wajan warware rikicin yankin na gabas ta tsakiya
Wannan tashin hankali kuwa na ƙara tsananta ne duk da irin yunƙurin da ƙasashen duniya suke yi na warware rikicin da gauggawa kafin ya kai ga caɓewa;sakatariyar harkokin wajan Amirka Hillary Clinton wacce ta katse wata ziyara aiki da ta ke a yankin Asiya domin zuwa Isira'ilan ta ce suna ƙoƙarin shawo kan lamarin.Ta ce ''A cikin kwanaki na gaba masu zuwa AmIrka tare da sauran ƙauwanta zasu yi aiki tare domin samar da zaman lafiya a Isira'ila da ma yankin baki ɗaya tare da samar da hanyoyin tabbatar da tsaro da kuma yanci walwala a Gaza akan yarjejenia zaman lafiyar da za a cimma.''A rana ta takwas na faɗan da ake yi falasɗiniyawa a ƙalla 138 suka mutu a cikin su yara guda 34, yayin da Yahudawa guda biyar suka cikka.
Isira'ila ta ce za ta ƙara tsanata kai hare hare indan ba a yi sulhu ba
Duk da ma cewar batun cimma yarjejeniya dakatar a buɗe wuta shi ne a yanzu aka mayar da hankali a kai ta ko wane hali amma fa kungiyar Hamas da alama abin da ya fi damun ta shi ne kawo ƙarshen mammayar da Isiara'ila ke a yankin Gaza wanda ta killace abin da ake gani zai sa da wahala a kai ga samun wata yarjejeniya:
Fraministan Benjamin Netanyahu wanda ake kyautata zaton cewar zai sake samun nasara a zaɓen yan majalisun dokokin da za a gudanar cikin watan gobe ya ce ya na fatan za a cimma wata yarjejeniya mai ɗorewa akan batun Gazar, wanda kuma ya e idan har haka ya gaggara to kam Isira'ila, baza ta yi wata wata ba wajan ci gaba da kai harin mafi muni ga Hamas. Ya ce ''idan da hali na samun daidaituwa ta hanyoyin diflomasiya ya ce muna marhaba da haka kuma mun fi son haka, ya ce amma allah kuli hali Isira'ila zata kare al'ummarta da yancinta.''
Tun da farko an yi tsamanin tun a daran jiya Za a kai ga cimma yarjejeniya a ƙarƙashin jagoranci Mohammed Morsi na ƙasar Masar mai shiga tsakanin, amma kuma har kawo yanzu babu wasu baiyanai da aka samu dangane da abin da ya haifar da jinkiri amma kafin nan shugabannin na ci gaba da ɗaga murya tare da yin kira ga sasan biyu da su ba da haɗin kai wajan daidaita rikicikin.Fafaroma Benedicht na 16 ya yi gargadin cewar tashin hankali, da fitina ba zasu taɓa zama hanyoyin warware matsala ba , hasalima ga irin halin da aka shiga a yankin gabas ta tsakiya don a haka ya yi kira da a samar da hanyoyin tattaunawa don kawo ƙarshen faɗan.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto