1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila da Hamas sun cimma tsagaita wuta a Gaza

Abdourahamane Hassane
January 15, 2025

Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tare da sakin mutanen da ake garkuwa da su

Yankin zirin Gaza da yaki ya yi wa kaca kaca
Hoto: Tsafrir Abayov/AP/picture alliance

Jami'an Qatar da na Hamas sun ce sun cimma matsaya na tsagaita wuta a fadan da ake yi tsakanin Hamas da Israila

Firaministan Qatar Mohammed ben Abdelrahmane Al-Thani wanda ke shiga tsakani a tattaunawar, ya gana da tawagogin Hamas da na Isra'ila dabam-daban a birnin Doha

 jim kadan bayan ganawar firaministan ya ce an warware y'ar  takaddama da ta so hanna ruwa guda a tattaunawar, amma yanzu ya ce an samu daidaituwar baki

Yarjejeniyar dai ta tanadi dakatar da bude wuta nan take, tare da sako mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza