1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila da Hezbollah sun amince da tsagaita bude wuta-Trump

June 2, 2026

Trump ya ce an cimma matsayar tsagaita wuta bayan tattaunawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Hezbollah.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a lokacin da yake ganawa da sojojin kasar a birnin Qudus
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a lokacin da yake ganawa da sojojin kasar a birnin QudusHoto: Israeli Prime Minister Office/apaimages/IMAGO

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Isra'ila da Hezbollah sun amince da sabon daftarin yarjejeniyar tsagaita bude wuta bayan kwashe kwanaki ana gwabza yaki tsakanin bangarorin biyu, musamman a kudancin Beirut.

Karin bayani:Hezbollah ta yi watsi da shirin kwance mata damara

Trump ya ce a halin yanzu dakarun Isra'ila sun fara janyewa daga yankin Beirut kuma babu zancen sake kai farmaki tun bayan wayar tarho da suka yi da Mr. Netanyahu da kuma Hezbollah ta hanyar masu shiga tsakani.

Karin bayani:Hezbollah ta gargadi Lebanon kan tattaunawa da Isra'ila

Ya kara da cewa Hezbollah ta amince da tsagaita bude wuta nan take, kuma ba za ta sake kai wa Isra'ila hari ba. Kalaman Trump na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra'ila ta kaddamar da munanan hare-hare a kudancin Beirut, yayin da Hezbollah ta maida martani nan take, inda ta harba rokoki wasu yankuna da ke arewacin Isra'ila ciki har da birnin Haifa.