Dakatar da kai hari ta kasa a Zirin Gaza
October 25, 2023Fitacciyar mujallar nan ta Amurka wato Wall Street da ta ruwaito labarin ta bayyana cewa, Isra'ilan ta dauki wannan matakin ne, domin bai wa Washington damar shigar da makaman kariya daga makamai masu linzami ga sojojinta da ke yankin. Rahoton mujallar ya ce, Isra'ilan na tunanin ta bayar da damar kai kayan agajin jin-kai ga fararan hular da yaki ya rutsa da su a Zirin na Gaza. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, Amurka ta shawarci Tel Aviv ta dakatar da kaddamar da hare-haren ta kasa a yankin. A wani labarin kuma, firaministan Sweden Tobias Lennart Billström ya bayyana cewa mafita daya tilo ta kawo karshen rikicin Isra'ila da Falasdinu ita ce samar da kasashe biyu a yankin. Billström ya nunar da hakan ne, yayin wata hira da ya yi da tashar DW.